2 Chronicles 23:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yehohiyada da ’ya’yansa maza suka fitar da ɗan sarki suka sa rawani a kansa; suka miƙa masa alkawarin, suka kuma yi shelarsa a matsayin sarki. Suka shafe shi suka kuma tā da murya suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يٜىٰهُواْيِدَ يَڢِتَرْدَ يُواْوَشْ، طَنْ سَرْكِے، يَسَا مَسَ هُولَرْ مُلْكِ؞ سَيْ يَمِيڧَ مَسَ تَكَرْدَرْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ، عَكَ سَنَرْ دَشِ سَرْكِے؞ سَيْ يٜىٰهُواْيِدَ تَرٜىٰدَ یَیَنْسَ مَظَا سُكَ نَطَشِ سَرْكِے، سَيْ مُتَنٜىٰ سُكَ طَغَ مُرْيَ سُكَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، يَا سَرْكِے!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya kawo ɗan sarkin, ya sa masa kambi, ya ba shi dokoki goma, aka yi shela aka ce shi ne sarki. Yehoyada da 'ya'yansa maza suka naɗa shi, suka ce, “Ran sarki ya daɗe!”