2 Chronicles 23:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَتَدُوبَ سَيْ تَغَ سَابُوانْ سَرْكِے أَڟَيٜىٰ عِنْدَ سَرْكِے يَكَنْ ڟَيَ كُسَدَ غِنْشِڧِنْ غِدَنْ تَڧُواْڢَرْ شِغَ؞ سَوْرَنْ شُوغَبَنِّ دَ مَاسُ بُوشٜىٰ بُوشٜىٰنْ كَكَكِ سُنْ كٜىٰوَيٜىٰشِ، مُتَنٜىٰ دَغَ كُواْعِنَ عَڧَسَرْ سُنَ مُرْنَ سُنَ بُوسَ كَكَكِ؞ مَوَاڧَ دَ كَايَنْ كَطٜىٰ كَطٜىٰنْسُ سُنَ جَغُواْرَنْ بِكٍ؞ سَعَدَّ أَتَلِيَ تَغَ حَكَ، سَيْ تَيَيَّاغٜىٰ رِيغُنَنْتَ تَيِ إِيهُ تَنَ ثٜىٰوَ «أَنْثِ أَمَانَتَ! أَنْثِ أَمَانَتَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da ta duba, sai ga sarki yana tsaye wajen ginshiƙin bakin ƙofa, ga shugabanni da masu busa ƙaho kewaye da sarkin. Dukan jama'a suna murna, suna busa ƙaho, mawaƙa kuma da kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushensu, suna shugabancin shagalin. Sai Ataliya ta yayyage tufafinta ta ce, “Tawaye! Tawaye!”