2 Chronicles 23:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan mutane suka tafi haikalin Ba’al suka rurrushe shi. Suka farfashe bagadan da gumakan, suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagadan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ سُكَ تَڢِے غِدَنْ بَعَلْ، سُكَ رُشٜىٰشِ؞ سُكَ كُمَ رُشٜىٰ بَغَدٜىٰنْسَ دَ غُمَكَنْسَ، سُكَ كُمَ كَشٜىٰ مَتَّنْ، ڢِرِسْتِ نَ بَعَلْ، أَغَبَنْ بَغَدٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dukan jama'a suka tafi gidan Ba'al, suka rushe shi, suka kuma ragargaza bagadansa, da siffofinsa. Suka kashe Mattan, firist ɗin Ba'al, a gaban bagadan.