2 Chronicles 23:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰهُواْيِدَ يَسَا لَوِيَاوَنْ دَسُكٜىٰ ڢِرِسْتُواْثِے عَيْكِنْ لُورَ دَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ سُونٜىٰ سَرْكِے دَاوُدَ يَشِرْيَ سُمِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا غَ يَهْوٜىٰهْ ، كَمَرْ يَدَّ عَكَ ڟَارَا أَ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى؞ ذَاسُ كُمَيِ وَاڧُواْڧِ دَ ڢَضٍ ثِكِ كَمَرْ يَدَّ دَاوُدَ يَعُمَرْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yehoyada kuma ya sa matsaran da za su yi tsaron Haikalin Ubangiji a ƙarƙashin ikon firistoci, Lawiyawa, waɗanda Dawuda ya shirya don su lura da Haikalin Ubangiji, su miƙa hadayu na ƙonawa ga Ubangiji, yadda aka rubuta a Attaura ta Musa, da murna da waƙa kamar yadda Dawuda ya shirya.