2 Chronicles 23:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, manyan gari, shugabannin mutane da dukan mutanen ƙasar tare da shi ya saukar da sarki daga haikalin Ubangiji. Suka shiga fada ta Ƙofar Bisa suka kuma zaunar da sarki a kujerar sarauta,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰهُواْيِدَ يَسَا شُوغَبَنِّنْ ڧُنْ‌غِيَرْ سُواْجُواْجِ طَرِے دَ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰ دَ شُوغَبَنِّنْ غَرِنْ دَ دُكَنْ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ، سُكَيِ رَكِيَرْ سَرْكِے دَغَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ سُكَبِے تَڧُواْڢَرْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ وَدَّ تَكٜىٰ أَوُرِے مَڢِے ڟَيِ سُكَ شِغَ غِدَنْ سَرْكِے، سُكَ كُمَسَا سَرْكِے يَذَوْنَ عَكَنْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya sa shugabanni, da dattawa, da masu mulki, da dukan jama'ar ƙasar, suka rufa wa sarki baya, daga Haikalin Ubangiji suka bi ta Ƙofar Bisa zuwa fādar sarki. Suka zo suka zaunar da sarki a gadon sarauta.