2 Chronicles 23:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دُكَنْسُ سُكَ تَارُ أَ غِدَنْ اللَّهْ سُكَيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَ سَرْكِنْ؞ سَعَنً يٜىٰهُواْيِدَ ڢِرِسْتِ يَثٜىٰ «غَا طَنْ سَرْكِے! بَرِ يَذَمَ سَرْكِے كَمَرْ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا ثٜىٰوَ یَیَنْ دَاوُدَ نٜىٰ كَطَيْ ذَاسُيِ مُلْكِنْمُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dukan taron suka yi wa sarki alkawari, a Haikalin Allah. Yehoyada ya ce musu, “Wannan shi ne ɗan sarki, sai ya ci sarauta kamar yadda Ubangiji ya faɗa a kan 'ya'yan Dawuda, maza.