2 Chronicles 24:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَتَتَّارَ ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا دُكَ يَثٜىٰ مُسُ «كُتَڢِے ثِكِنْ غَرُضُوً يَهُودَ، كُتَارَ كُطَطٜىٰ نَشٜىٰكَرَا شٜىٰكَرَا دَغَ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا، دُواْمِنْ كُڠَرَ غِدَنْ اللَّهْ نْكُ؞ كُيِ سَوْرِ!» عَمَّا لَوِيَاوَنْ سُكَڧِ يِنْ سَوْرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya tattara firistoci da Lawiyawa, ya ce musu, “Ku shiga biranen Yahuza, ku tattara kuɗi daga dukan Isra'ilawa domin a riƙa gyaran Haikalin Ubangijinku kowace shekara. Ku hanzarta al'amarin fa.” Amma Lawiyawa ba su hanzarta ba.