2 Chronicles 25:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Amaziya ya sallame rundunonin da suka zo daga Efraim, ya kuma mayar da su gida. Suka husata da Yahuda suka koma gida da fushi sosai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَمَظِيَ يَسَلَّمِ مُتَنٜىٰنْ إِڢْرَيِمْ وَطَنْدَ يَبِيَسُ كُطِنْ هَيَ دُواْمِنْ سُكُواْمَ غِدَا؞ سَيْ سُكَيِ ڢُشِے دَ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ، سُكَ كُوَ كُواْمَ غِدَا ثِكِنْ ذَاڢِنْ ڢُشِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Amaziya ya sallami rundunar sojojin da suka zo daga Ifraimu, su koma gida. Sai suka yi fushi da Yahuza ƙwarai suka koma gida cike da hasala mai zafi.