2 Chronicles 25:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ana cikin haka, sai rundunar da Amaziya ya mai da su gida, waɗanda ba a bari suka tafi yaƙin ba, suka kai wa garuruwan Yahuda daga Samariya zuwa Bet-Horon hari. Suka kashe mutane dubu uku suka kwashe ganima mai yawan gaske.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا مُتَنٜىٰنْ إِڢْرَيِمْ وَطَنْدَ سَرْكِے أَمَظِيَ يَسَلَّمٜىٰسُ يَهَنَاسُ ذُوَا يَاڧِنْ، سُكَ ڢَاطُواْوَ غَرُضُوً يَهُودَ دَ يَاڧِ، تُنْدَغَ سَمَرِيَ حَرْ ذُوَا بٜىٰتْ حُواْرُوانْ؞ سُكَ كَشٜىٰ مُتَنٜىٰ دُبُو عُكُ، سُكَ ݣُوشِ كَايَ مَاسُيَوَ دَغَ وُرِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma sojojin rundunar da Amaziya ya sallama, bai yarda su tafi yaƙi tare da shi ba, suka faɗa wa biranen Yahuza da yaƙi, tun daga Samariya har zuwa Bet-horon, suka kashe mutum dubu uku (3,000), a cikinsu suka kwashe ganima mai yawan gaske.