2 Chronicles 25:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Amaziya ya dawo daga kisan mutanen Edom, sai ya dawo da allolin mutanen Seyir. Ya kafa su a matsayin allolinsa, ya rusuna musu, ya kuma miƙa musu hadayun ƙonawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ أَمَظِيَ يَكُواْمَ دَغَ كِسَنْ عٜىٰدُواْمَاوَا، سَيْ يَكَٰوُاْ غُمَكَنْسُ وَطَنْدَ يَݣُوسُواْ؞ يَأَجِيٜىٰسُ سُذَمَ غُمَكَنْسَ، يَيِ مُسُ سُجَّدَ، يَكُمَ مِيڧَ مُسُ هَدَايُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Amaziya ya komo daga kisan Edomawa, sai ya kwaso gumakan mutanen Seyir, ya ajiye su su zama gumakansa, ya yi musu sujada, ya kuma miƙa musu hadaya.