2 Chronicles 25:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kwashe dukan zinariya da azurfa da dukan kayayyakin da aka samu a haikalin Allah waɗanda suke a ƙarƙashin kulawar Obed-Edom, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَڨُوثٜىٰ دُكَنْ ظِينَارِيَ دَ أَظُرْڢَا دَ دُكَنْ كَايَنْ غِدَنْ اللَّهْ وَطَنْدَ عَكَ دَنْڧَسُ أَ حَنُّنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ؞ يَكُمَ ڨُوثٜىٰ كَايَ مَاسُ دَرَجَ دَغَ غِدَنْ سَرْكِے، يَكُمَ ݣُوشِ مُتَنٜىٰنْ دَ ذَيْ رِڧٜىٰ سَيْ أَنْڢَنْشٜىٰسُ؞ سَيْ يَكُواْمَ سَمَرِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai ya kwashe dukan zinariya da azurfa, da dukan tukwane da tasoshi da aka samu a Haikalin Allah, waɗanda iyalin Obededom suke tsaro, da kaya masu daraja na gidan sarki, da waɗanda aka kamo cikin yaƙi, ya kawo Samariya.