2 Chronicles 25:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amaziya ya tambayi mutumin Allah ya ce, “Amma game da talenti ɗarin da na biya saboda waɗannan rundunonin Isra’ila fa?” Mutumin Allah ya amsa, “ Ubangiji zai ba ka fiye da wannan.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَمَظِيَ يَثٜىٰ وَمُتُمِنْ اللَّهْ «تُواْ، يَيَ ذَنْيِ دَ كُطِنْ أَظُرْڢَا كِلُواْ دُبُو عُكُ دَ طَرِے حُطُ وَنْدَ نَارِغَا نَا بَا سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؟» سَيْ مُتُمِنْ اللَّهْ يَثٜىٰ مَسَ « يَهْوٜىٰهْ يَنَدَ إِيكُواْ يَبَاكَ أَبِنْدَ يَڢِ وَنَّنْ يَوَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amaziya kuwa ya ce wa annabin Allah, “To, me za mu yi yanzu game da azurfar da muka ba sojojin Isra'ila?” Sai annabin Allah ya amsa ya ce, “Ubangiji yana da iko ya ba ka fiye da haka.”