2 Chronicles 26:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَكُمَيِ غِنٜىٰ غِنٜىٰ مَاسُ ڟَيِ أَدَاجِ، يَحَڧَ رِجِيُواْيِ مَاسُيَوَ، سَبُواْدَ يَنَدَ شَانُو سُواْسَيْ عَثِكِنْ يَنْكِنْ ڧأَنَانً تُدَّيْ دَ ثِكِنْ ڢِيلَيٜىٰ؞ يَنَ دَ مَنُواْمَ دَ مَاسُ لُورَ دَ غُواْنَكِنْ إِنَبِنْسَ نَكَنْ تُدَّيْ دَ نَڢِيلَيٜىٰنْ غُواْنَكِ مَاسُ بَادَ أَمْڢَانِ ڨُورَيْ، غَمَا شِے مَيْ سُواْ يِنْ نُواْمَ نٜىٰ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma gina hasumiyai a jeji, ya haƙa tafukka masu yawa, saboda yana da garkunan dabbobi da yawa, da waɗanda suke Shefela da waɗanda suke a filin tudu. Yana kuma da manoma da masu yi wa kurangar inabi aski a tuddai, da wajen ƙasashe masu dausayi, gama shi mai son noma ne ƙwarai.