2 Chronicles 26:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Uzziya ya kasance da gogaggun mayaƙa, a shirye su fito ɓangarori-ɓangarori bisa ga yawansu yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’asehiya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin fadawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عُزِّيَ يَنَدَ ڧُنْغِيُواْيِنْ سُواْجُواْجِ مَاسُ عِيَ يَاڧِ، سُنَانَنْ ڧُنْغِيَ ڧُنْغِيَ؞ أَنْڟَارَسُ كَمَرْ يَدَّ يٜىٰيِيٜىٰلْ مَرُبُوثِنْ سَرْكِے دَ مَعَسٜىٰيَ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِ سُكَ لِسَّڢْتَاسُ؞ سُنْيِ وَنَّنْ عَڧَرْڧَشِنْ جَغُواْرَنْثِنْ هَنَنِيَ بَبَّنْ سُواْجَنْ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Har yanzu kuma, Azariya yana da rundunar sojoji waɗanda suka iya yaƙi ƙungiya ƙungiya, yadda Yehiyel magatakarda, da Ma'aseya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin 'yan majalisar sarki.