2 Chronicles 26:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَعَدَّ عُزِّيَ يَغَ يَيِ ڧَرْڢِے سُواْسَيْ، سَيْ يَڢَارَ يِنْ غِرْمَنْ كَيْ، وَنْدَ يَجَٰوُاْ مَسَ هَلَّكَ؞ غَمَا يَيِ رَشِنْ أَمِنْثِ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسَ، حَرْ يَشِغَ هَيْكَلِنْ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْ يَڧُواْنَ تُرَارٜىٰ عَكَنْ بَغَدٜىٰ دَ كَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma sa'ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.