2 Chronicles 26:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka kalubalance shi suka ce, “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙone turare ga Ubangiji. Wannan aikin firistoci zuriyar Haruna ne, waɗanda aka tsarkake don ƙone turare. Ka bar wuri mai tsarki, gama ka kasance marar aminci; kuma Ubangiji Allah ba zai girmama ka ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ ڢُسْكَنْثٜىٰ شِ سُنَ ثٜىٰ مَسَ «بَ دَيْدَيْ بَنٜىٰ، عُزِّيَ، كَڧُواْنَ تُرَارٜىٰ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞ وَنَّنْ عَيْكِنْ ڢِرِسْتِنٜىٰ نَظُرِيَرْ هَٰرُونَ، وَطَنْدَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ مُسَمَّنْ دُواْمِنْ وَنَّنْ عَيْكِنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ؞ كَڢِتَ دَغَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِنَّنْ، غَمَا كَايِ رَشِنْ أَمِنْثِ؞ وَنَّنْ بَذَيْ كَٰوُاْ مَكَ طَوْكَكَ دَغَ وُرِنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ بَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka hana sarki Azariya, suka ce masa, “Ba aikinka ba ne, Azariya, ka ƙona turare ga Ubangiji, wannan aikin firistoci ne, 'ya'yan Haruna, waɗanda aka keɓe su don ƙona turare. Fita daga wurin nan mai tsarki, gama ka yi kuskure, ba za ka sami daraja daga wurin Ubangiji Allah ba.”