2 Chronicles 26:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Uzziya wanda yake da farantin wuta a hannunsa a shirye don ƙone turare, ya husata. Yayinda yake fushi da firistocin a gabansu a gaban bagaden turare a haikalin Ubangiji, sai kuturta ta faso a goshinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عُزِّيَ يَيِ ڢُشِے؞ يَنَ كُوَ ڟَيٜىٰ كُسَدَ بَغَدٜىٰنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ ثِكِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، يَنَ رِڧٜىٰ دَ ݣُونُواْ نَڧُواْنَ تُرَارٜىٰ أَ حَنُّنْسَ؞ سَعَدَّ يَكٜىٰ ڢُشِنْ، سَيْ ثُوتَرْ ڢَتَ تَٻُلُّواْ مَسَ أَغُواْشِ أَعِدُوانْ ڢِرِسْتُواْثِنْ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ أَغَبَنْ بَغَدٜىٰنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Azariya ya yi fushi, a lokacin kuwa yana riƙe da farantin ƙona turare a hannunsa, sa'ad da ya yi fushi da firistocin, sai kuturta ta faso a goshinsa, a nan gaban firistocin a cikin Haikalin Ubangiji, wajen bagaden ƙona turare.