2 Chronicles 26:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Uzziya ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi kusa da su a fili don binnewar da take ta sarakuna, domin mutane sun ce, “Yana da kuturta.” Sai Yotam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عُزِّيَ يَكُواْمَ غَ كَاكَنِّنْسَ، عَكَ بِنّٜىٰشِ كُسَدَ وُرِنْ بِنّٜىٰ سَرَاكُنَ؞ عَمَّا بَعَبِنّٜىٰشِ عَثِكِنْسُبَ غَمَا مُتَنٜىٰ سُنَ ثٜىٰوَ «شِے مَيْ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِنٜىٰ؞» سَيْ طَنْسَ يُواْتَمْ يَغَاجٜىٰشِ يَذَمَ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Azariya ya rasu, suka binne shi tare da kakanninsa a hurumin sarakuna, gama suka ce, “Shi kuturu ne.” Sai Yotam ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.