2 Chronicles 27:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yotam ya yi yaƙi da sarkin Ammonawa ya kuma ci su. A wannan shekara Ammonawa suka biya shi haraji talenti ɗari na azurfa, garwan alkama dubu goma da kuma garwa dubu goma na sha’ir. Ammonawa suka kawo masa wannan kuma a shekara ta biyu da ta uku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَيِ يَاڧِ دَ أَمُّواْنَاوَا يَثِ نَصَرَا؞ أَ شٜىٰكَرَرْ نَنْ يَسَا أَمُّواْنَاوَا سُبِيَ هَرَاجِ نَأَظُرْڢَا، كِلُواْ دُبُو عُكُ دَ طَرِے حُطُ دَ نَأَلْكَمَ تُوانْ دُبُو طَيَ دَ نَهَڟِنْ بَلٜىٰ تُوانْ دُبُو طَيَ؞ حَكَ أَمُّواْنَاوَا سُكَيِ تَبِيَ أَ شٜىٰكَرَا تَبِيُ دَ تَ عُكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya yi yaƙi da Sarkin Ammonawa, ya kuwa ci nasara, har Ammonawa suka ba shi talanti ɗari na azurfa a wannan shekara, da alkama mudu dubu goma (10,000) da sha'ir mudu dubu goma (10,000). Haka Ammonawa suka yi ta biya a shekara ta biyu da ta uku.