2 Chronicles 28:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka ce, “Dole ku kawo waɗannan ’yan kurkukun a nan, ko kuwa za ku yi laifi a gaban Ubangiji. Kuna niyya ku ƙara ga zunubinmu da kuma laifinmu? Gama laifinmu ya riga ya yi yawa, kuma fushinsa mai tsanani yana a kan Isra’ila.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَثٜىٰ «بَذَاكُ شِغُواْ دَ وَطَنَّنْ دَ كُكَ كَمُواْ دَغَ وُرِنْ يَاڧِ بَ، غَمَا وَنَّنْ ذَيْ جَٰوُاْ مَنَ لَيْڢِے أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ كُنَ سُواْ كُڧَارَ مَنَ لَيْڢِے دَ ذُنُوبِ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ؟ كُواْ يَنْذُ مَا ڢُشِنْ يَهْوٜىٰهْ يَا رِغَا يَايِ ذَاڢِ عَكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka ce musu, “Kada ku shigo nan da waɗanda kuka kamo daga wurin yaƙin, gama so kuke ku jawo mana laifi a gaban Ubangiji, a kan manyan zunuban da muka riga muka yi, gama Ubangiji yana fushi da Isra'ila ƙwarai.”