2 Chronicles 28:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَكُمَ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ عَثِكِنْ ݣُورِنْ هِنُّوامْ، يَمِيڧَ یَیَنْسَ مَظَا هَدَايَ ثِكِنْ وُتَا؞ يَنَ بِنْ حَلِنْ مَاسُ بَنْ ڨَمَ نَڧَبِيلُنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَكُواْرَ دَغَ ڧَسَرْ دُواْمِنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُذَوْنَ أَوُرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Banda haka ma ya ƙona turare a kwarin ɗan Hinnom, ya ƙone 'ya'yansa maza bisa ga ƙazantattun al'adun al'ummai, waɗanda Ubangiji ya kore su daga gaban mutanen Isra'ila.