2 Chronicles 28:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus. Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسَ يَبَاشٜىٰشِ أَ حَنُّنْ سَرْكِنْ سُورِيَ؞ سُرِيَاوَا سُكَثِ شِ دَ يَاڧِ، عَكَ ݣُوشِ مُتَنٜىٰنْسَ دَيَوَ ذُوَا دِمَشْڧُ؞ يَهْوٜىٰهْ يَا كُمَ بَاشٜىٰشِ أَ حَنُّنْ سَرْكِے ڢٜىٰكَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، إِسْرَٰٓءِيلَاوَا كُوَ سُكَ كَشٜىٰ سُواْجُواْجِنْ يَهُودَ دَيَوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya bashe shi a hannun Sarkin Suriya. Suka ci shi da yaƙi suka kama mutanensa da yawa, suka kai su Dimashƙu. Aka kuma bashe shi a hannun Sarkin Isra'ila, wanda ya ci shi da yaƙi, ya kashe masa mutane masu yawa.