2 Chronicles 29:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka fara tsarkakewar a rana ta farko na farkon wata, a rana ta takwas na watan kuwa suka kai shirayin Ubangiji. Karin kwana takwas kuma suka tsarkake haikalin Ubangiji kansa, suka gama a rana ta goma sha shida na farkon wata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَ تَڢَرْكُواْ أَوَتَنْ طَيَ، سُكَ ڢَارَ عَيْكِنْ ڟَرْكَكٜىٰوَرْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، سَعَنً أَ رَانَ تَتَݣُوسْ سُكَ كَيْ ڢِيلِنْ غَبَنْ غِدَنْ؞ سُكَ ڧَارَ وَطَنْسُ ݣُونَكِے تَݣُوسْ سُنَ ڟَرْكَكٜىٰوَرْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ وَنَّنْ يَسَا سُكَ كَمَّلَ أَ رَانَ تَغُواْمَشَا شِدَ غَ وَتَنْ طَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A rana ta fari a watan ɗaya suka fara aikin tsarkakewar. A rana ta takwas ga watan suka kai shirayin Ubangiji da aikin, kwana takwas suka ɗauka domin tsabtace Haikalin Ubangiji, a ranar sha shida ga watan ɗaya suka gama.