2 Chronicles 29:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan suka tafi wurin Sarki Hezekiya suka faɗa masa, “Mun tsarkake haikalin Ubangiji gaba ɗaya, bagaden ƙone hadaya tare da dukan kayayyakinsa, da tebur don shirya tsarkaken burodi, tare da dukan kayayyakinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتُواْثِنْ سُكَ تَڢِے وُرِنْ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ أَغِدَنْ سَرْكِے؞ سَيْ سُكَثٜىٰ مَسَ «مُنْ ڟَبْتَثٜىٰ دُكَنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ دَ بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا، تَرٜىٰدَ دُكَنْ كَايَنْ عَيْكِنْسَ دَ تٜىٰبُرِنْ غُرَاسَرْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ، تَرٜىٰدَ كَايَنْ عَيْكِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka tafi wurin sarki Hezekiya suka ce, “Mun tsabtace Haikalin Ubangiji duka, da bagaden hadayar ƙonawa tare da dukan tasoshi, da tukwane, da teburin gurasar ajiyewa da kuma dukan kayayyakin da yake ciki.