2 Chronicles 29:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka kawo bijimai bakwai, raguna bakwai, bunsurai bakwai da kuma awaki mata bakwai a matsayin hadaya don zunubi domin masarauta, domin wuri mai tsarki da kuma domin Yahuda. Sarki ya umarce firistoci, zuriyar Haruna, su miƙa waɗannan a bagaden Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ كَٰوُاْ بِجِمَيْ بَݣَويْ دَ رَغُنَ بَݣَويْ دَ یَنْ رَغُنَ بَݣَويْ دَ بُنْسُرَيْ بَݣَويْ؞ دُكَنْ دَبُّواْبِنَّنْ أَنْمِيڧَسُ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِنْ مُلْكِ دَ نَمُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ يَهُودَ دَ كُمَ ڟَبْتَثٜىٰوَرْ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے؞ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ يَعُمَرْثِ ڢِرِسْتُواْثِے، وَتُواْ ذُرِيَرْ هَٰرُونَ، سُمِيڧَ هَدَايَ عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka kawo bijimai bakwai, da raguna bakwai, da 'yan raguna bakwai, da bunsurai bakwai, domin yin hadaya don zunubi saboda mulkin, da Wuri Mai Tsarki, da kuma Yahuza. Sai ya umarci firistoci, wato 'ya'yan Haruna, maza, su miƙa su a kan bagaden Ubangiji.