2 Chronicles 29:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka suka yayyanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin suka yayyafa a kan bagade. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka kuma suka yanka ’yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ يَنْكَ بِجِمَنْ، ڢِرِسْتُواْثِے كُوَ سُكَ كَرْٻِ جِنِنْ، سُكَ يَيَّڢَا عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ؞ سُكَ كُمَ يَنْكَ رَغُنَ سُكَ يَيَّڢَا جِنِنْ عَبَغَدٜىٰنْ؞ سَعَنً سُكَ يَنْكَ یَنْ رَغُنَ سُكَ يَيَّڢَا جِنِنْ عَبَغَدٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka yanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin, suka yayyafa a jikin bagaden. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka nan kuma suka yanka 'yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden.