2 Chronicles 29:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ هٜىٰزٜىٰكِيَ يَعُمَرْتَ أَ مِيڧَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا عَكَنْ بَغَدٜىٰ؞ سَعَدَّ عَكَ ڢَارَ مِيڧَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا، سَيْ عَكَ ڢَارَ رٜىٰرَ وَاڧُواْڧِنْ يَبُواْ غَ يَهْوٜىٰهْ ، عَكَ بُوسَ كَكَكِ، تَرٜىٰدَ سَوْرَنْ كَايَنْ بُوشٜىٰ بُوشٜىٰ دَ كَطٜىٰ كَطٜىٰ نَ سَرْكِے دَاوُدَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawar a bisa bagaden. Sa'ad da aka fara miƙa hadaya ta ƙonawa, sai aka fara raira waƙa ga Ubangiji, aka busa ƙaho, sai sauran masu kayan kaɗe-kaɗe da na bushe-bushe na Dawuda, Sarkin Isra'ila, suka kama.