2 Chronicles 29:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yawan hadayun ƙonawan da taron suka kawo, bijimai saba’in ne, raguna ɗari da kuma bunsurai ɗari biyu, dukansu kuwa domin hadayun ƙonawa ga Ubangiji ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَوَنْ هَدَايُنْ دَ تَارُوانْ جَمَعَ سُكَ كَٰوُاْ سُونٜىٰ، بِجِمَيْ سَبَعِنْ دَ رَغُنَ طَرِے طَيَ دَ یَنْ رَغُنَ طَرِے بِيُ نٜىٰ؞ أَنْ مِيڧَ دَبُّواْبِنَّنْ دُكَ دُواْمِنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jimillar hadayu na ƙonawa waɗanda taron suka kawo, su ne bijimai saba'in, da raguna ɗari, da 'yan raguna ɗari biyu, waɗannan duka kuwa don hadaya ne ta ƙonawa ga Ubangiji.