2 Chronicles 29:34 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firistoci fa, suka kāsa sosai don fiɗan dukan dabbobin da za a miƙa don hadayun ƙonawa; saboda haka ’yan’uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا ڢِرِسْتُواْثِنْ بَسُيِيَوَبَ، سُنْ كَاسَ دُواْمِنْ عَيْكِنْ ڢِطَ دُكَنْ دَبُّواْبِنْ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا؞ سَيْ یَنْعُوَنْسُ لَوِيَاوَا سُكَ تَيْمَكٜىٰسُ حَرْ سُكَ غَمَ عَيْكِنْ، سَوْرَنْ ڢِرِسْتُواْثِے كُمَ سُكَ كَمَّلَ ڟَرْكَكٜىٰ كَنْسُ؞ لَوِيَاوَا سُنْ عِيَ تَيْمَكٜىٰسُ عَيْكِنْ غَمَا سُنْڢِے ڢِرِسْتُواْثِنْ وَجٜىٰنْ تَبَّتَرْ دَ ڟَرْكَكٜىٰوَرْ كَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma su firistoci kima ne, don haka sun kāsa fiɗa dukan dabbobin da za a miƙa su hadaya ta ƙonawa. Sai 'yan'uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu.