2 Chronicles 29:35 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Aka kasance da hadayun ƙonawa a yalwace, tare da kitsen hadayun salama da hadayun sha da suke tafe da hadayun ƙonawa. Saboda haka aka sāke kafa hidimar haikalin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَنْ دَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا مَاسُيَوَ، أَݣَويْ هَدَايُنْسُ نَشَا دَ كِڟٜىٰنْ هَدَايُ نَڠَرَنْ زُمُنْثِ؞ تَهَكَ عَكَ سَاكٜىٰ كَڢَ حِدِمَ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Banda hadayu masu yawa na ƙonawa da aka yi, akwai kuma kitse na hadaya ta salama, akwai kuma hadaya ta sha don kowace hadaya ta ƙonawa. Da haka fa aka maido hidimar Haikalin Ubangiji.