2 Chronicles 29:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka kulle ƙofofin shirayi, suka kuma kashe fitilu. Ba su ƙone turare ko su miƙa hadayun ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra’ila ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاكَنِّنْمُ سُنْ رُڢٜىٰ ڧُواْڢُواْڢِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، سُكَ كَشٜىٰ ڢِتِلُ؞ سُكَ دَيْنَ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ كُواْ مِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا عَثِكِنْ غِدَنْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun kuma rurrufe ƙofofin shirayi suka kashe fitilu, sun daina ƙona turare ko miƙa hadayun ƙonawa a Wuri Mai Tsarki ga Allah na Isra'ila.