2 Chronicles 3:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shirayin da yake gaban haikalin kuma kamun ashirin ne da ya nausa ya ƙetare, fāɗin ginin kuma tsayinsa kamu ashirin ne. Ya shafe cikin da zinariya zalla.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَوْرٜىٰنْ دَيَكٜىٰ أَغَبَنْ غِدَنْ، ڢَاطِنْسَ دَيْدَيْ يَكٜىٰدَ ڢَاطِنْ غِدَنْ، وَتُواْ ڧَڢَا تَلَاتِنْ، ڟَيِنْسَ كُمَ ڧَڢَا طَرِے دَ تَمَٰنِنْ؞ عَكَ شَاڢٜىٰ ثِكِنْ طَاكِنْ ذَوْرٜىٰنْ دَ ظِينَارِيَ ظَلَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tsawon shirayi daga gaban Haikalin ya yi daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, sa'an nan tsayinsa kamu ɗari da ashirin. Aka shafe ciki da zinariya tsantsa.