2 Chronicles 3:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya gina Wuri Mafi Tsarki, tsawonsa daidai da fāɗin haikalin. Tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuwa kamu ashirin. Ya shafe cikin da talenti ɗari shida na zinariya zalla.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
طَاكِ نَثِكِ، وَنْدَ عَكٜىٰثٜىٰ دَشِ وُرِے مَڢِے ڟَرْكِے، ڟَوُانْ طَاكِنْ دَيْدَيْنٜىٰ دَ ڢَاطِنْ غِدَنْ، وَتُواْ ڧَڢَا تَلَاتِنْ، ڢَاطِنْسَ كُمَ ڧَڢَا تَلَاتِنْ؞ عَكَ شَاڢٜىٰ بَنْغُواْ نَثِكِنْ وُرِے مَڢِے ڟَرْكِے دَ ظِينَارِيَ ظَلَّ وَدَّ تَكَيْ تُوانْ عَشِرِنْ دَبِيُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya gina Wuri Mafi Tsarki. Tsawonsa daidai da fāɗin Haikalin, wato kamu ashirin, fāɗinsa kuma kamu ashirin. Ya shafe shi da zinariya tsantsa, wadda jimillar nauyinta ta yi talanti ɗari shida.