2 Chronicles 30:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu na wata na biyu. Firistoci da Lawiyawa suka ji kunya suka tsarkake kansu, suka kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ يَنْكَ طَنْ ضَغُواْ نَبِكٍ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ أَ رَانَ تَغُواْمَشَا حُطُ غَ وَتَ نَبِيُ؞ سَيْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ لَوِيَاوَا وَطَنْدَ بَسُ ذَمَ مَرَرْ ڧَظَنْتَا بَ، سُكَجِ كُنْيَا، سُكَ ڟَرْكَكٜىٰ كَنْسُ، سَعَنً سُكَ كَٰوُاْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا سُكَ مِيڧَ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka yanka ɗan rago na Idin Ƙetarewa a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Suka sa firistoci da Lawiyawa su sha kunya, saboda haka sai suka tsarkake kansu, suka kawo hadayu na ƙonawa a Haikalin Ubangiji.