2 Chronicles 30:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko da yake yawancin mutanen da suka zo daga Efraim, Manasse, Issakar da Zebulun ba su tsarkake kansu ba, duk da haka suka ci Bikin Ƙetarewa, ba tare da bin abin da yake a rubuce ba. Amma Hezekiya ya yi addu’a dominsu cewa, “Bari Ubangiji, wanda yake nagari, yă gafarta wa kowa
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰ دَيَوَ وَطَنْدَ سُكَ ڢِتُواْ دَغَ ذُرِيَرْ إِڢْرَيِمْ دَ تَ مَنَسّٜىٰ دَ تَ إِسَّكَرْ دَ تَ ظٜىٰبُلُنْ بَسُ ڟَبْتَثٜىٰ كَنْسُبَ؞ دُكْدَهَكَ سُكَثِ عَبِنْثِنْ بِكٍ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ، كُواْدَيَكٜىٰ بَ دَيْدَيْ بَنٜىٰ بِسَغَ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى؞ عَمَّا سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ يَيِ مُسُ أَدُّعَ، يَثٜىٰ «بَرِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ أَلْحٜىٰرِ يَغَاڢَرْتَا وَكُواْوَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama akwai jama'a jingim, da yawa kuwa mutanen Ifraimu ne, da na Manassa, da na Issaka, da na Zabaluna, da ba su tsarkake kansu ba, duk da haka sun ci Idin Ƙetarewa ba yadda aka ƙayyade ba. Sai Hezekiya ya yi addu'a dominsu, yana cewa, “Ya Ubangiji mai alheri, ka gafarta wa ko wanne