2 Chronicles 30:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Isra’ilawan da suka kasance a Urushalima suka yi Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai da farin ciki mai girma, yayinda Lawiyawa da firistoci suke rera ga Ubangiji kowace rana, haɗe da kayan kiɗin yabon Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنْدَ سُكَ تَڢِے عُرُوشَلِيمَ سُكَيِ بِكٍ غُرَاسَرْ مَرَرْ يِسْتِ حَرْ ݣُونَ بَݣَويْ دَ ڢَضٍ ثِكِ مَيْ يَوَ؞ لَوِيَاوَا دَ ڢِرِسْتُواْثِے سُكَ يَبِے يَهْوٜىٰهْ كُواْوَثٜىٰ رَانَ، سُنَ رٜىٰرَ وَاڧُواْڧِ دَ كَايَنْ كَطٜىٰ كَطٜىٰ مَاسُ ڧَارَ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jama'ar Isra'ila waɗanda suke a Urushalima kuwa sun yi idin abinci marar yisti da murna mai yawa, har kwana bakwai. Lawiyawa kuma da firistoci suka yabi Ubangiji kowace rana, suna raira waƙa da iyakar ƙarfinsu ga Ubangiji.