2 Chronicles 31:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bugu da ƙari, suka ba da rabo ga maza ’yan shekaru uku ko fiye waɗanda sunayensu suna a tarihin zuriya, dukan waɗanda ba za su iya shiga haikalin Ubangiji su yi ayyukansu na kullum ba, bisa ga nawayarsu da kuma sassansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ كُمَ رَرَّبَ ݣَوْتَيْ غَ دُكَنْ مَظَا مَاسُ شٜىٰكَرَا عُكُ ذُوَا سَمَ وَطَنْدَ عَكَ رُبُوتَ سُونَيٜىٰنْسُ عَثِكِنْ تَارِيحِنْ أَصَلِنْ لَوِيَاوَا، وَتُواْ دُكْ وَطَنْدَ ذَاسُ شِغَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ كُلُّمْ دُواْمِنْ يِنْ حِدِمَ بِسَغَ ڟَارِنْ عَيْكِنْ ڧُنْغِيَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
da su kuma waɗanda aka rubuta bisa ga asali, 'yan samari masu shekara uku zuwa sama, duk dai waɗanda za su shiga Haikalin Ubangiji don yin hidima, kamar yadda aka tsara, bisa ga matsayinsu yadda aka karkasa su.