2 Chronicles 31:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki ya ba da taimako daga mallakarsa domin hadayun ƙonawa, safe da yamma da kuma don hadayun ƙonawa a Asabbatai, Sabon Wata da kuma ƙayyadaddun bukukkuwa kamar yadda yake a rubuce a cikin Dokar Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَكُمَ بَادَ نَاسَ تَيْمَكُواْ نَأَبِنْ يِنْ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا، وَطَنْدَ عَكَنْيِ كُواْوَثٜىٰ سَاڢِيَ دَ يَمَّ دَ كُمَ رَانَكُنْ هُوتُ تَمَكُواْ دَ نَ سَابُوانْ وَتَ دَ كُمَ رَانَكُنْ بُكُكُوَنْ دَ عَكَ ڟَارَا، كَمَرْ يَدَّ عَكَ عُمَرْتَ أَ كُواْيَرْوَرْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga dukiyarsa kuma ya ba da taimako na abin yin hadayun ƙonawa, wato hadayun ƙonawa na safe da na maraice, da hadayun ƙonawa na ranakun Asabar, da na amaryar wata, da na ƙayyadaddun idodi, kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Ubangiji.