2 Chronicles 32:31 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma da masu mulkin Babilon suka aika da jakadu su tambaye shi game alamar da ta faru a ƙasar, Allah ya rabu da shi don yă gwada shi don yă kuma san kome da yake cikin zuciyarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا لُواْكَثِنْ دَ یَنْ عَيْكَ دَغَ سَرْكِنْ بَابِيلَ سُكَ كَٰوُاْ زِيَارَ عَڧَسَرْ دُواْمِنْ سُبِنْثِكَ عَيْكِنْ بَنْ مَامَاكِنْ دَيَڢَرُ عَڧَسَرْ، سَيْ اللَّهْ يَڨَلٜىٰشِ كُرُمْ دُواْمِنْ يَڠُودَاشِ، يَسَنْ دُكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ أَ ذُوثِيَارْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kan 'yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al'ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.