2 Chronicles 32:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ دَ يَنَدَ سُواْجُواْجِ مَاسُيَوَ، سُنَدَ إِيكُواْ نَجِكِے نٜىٰ كَوَيْ، عَمَّا مُو مُنَدَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْمُ مَيْ تَيْمَكُوانْمُ، شِينٜىٰ ذَيْ يِيَاڧِ دُواْمِنْمُ!» مُتَنٜىٰ سُكَ سَامِ ڧَرْڢَڢَاوَا سُواْسَيْ دَ وَنَّنْ مَغَنَ تَسَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ نَ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hannun mutum yake tare da shi, amma mu Ubangiji Allahnmu yake tare da mu, domin ya taimake mu, ya yi yaƙi dominmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuza.