2 Chronicles 32:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga baya, sa’ad da Sennakerib sarkin Assuriya da dukan mayaƙansa suke kwanto wa Lakish, sai ya aiki hafsoshinsa da wannan saƙo wa Hezekiya sarkin Yahuda da kuma wa dukan mutanen Yahuda waɗanda suke can cewa,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَنَّنْ سَيْ سَرْكِے سٜىٰنَّكٜىٰرِبْ نَ أَسُّرِيَ يَعَيْكَ دَ یَنْ عَيْكَ ذُوَا عُرُوشَلِيمَ؞ أَ لُواْكَثِنَّنْ، شِ دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْسَ سُنَ كٜىٰوَيٜىٰ دَ بِرْنِنْ لَكِشْ دُواْمِنْ يَاڧِ؞ يَعَيْكَ وَ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ دَ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ دَ سَڧُواْ ثٜىٰوَ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan wannan sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya aika da barorinsa zuwa Urushalima, sa'an nan kuma ya kewaye Lakish da dukan mayaƙansa tare da shi, yana yaƙi da Hezekiya, Sarkin Yahuza, da dukan mutanen Yahuza waɗanda suke a Urushalima, yana cewa,