2 Chronicles 33:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ يَهْوٜىٰهْ يَسَا مَنْيَنْ سُواْجُواْجِنْ أَسُّرِيَ سُكَ كَامَ مَنَسّٜىٰ؞ سُكَسَا مَسَ ذُواْبٜىٰ أَهَنْثِ، سُكَ طَوْرَ شِ دَ سَرْڧُواْڧِنْ ڧَرْڢٜىٰ سُكَ كَيْ شِ بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.