2 Chronicles 33:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga baya ya sāke gina katangar waje na Birnin Dawuda, yamma da maɓulɓular Gihon a cikin kwari, har zuwa mashigin Ƙofar Kifi, ya kuma kewaye tudun Ofel; ya yi ta da tsayi sosai. Ya sa hafsoshin mayaƙa cikin dukan biranen katanga a Yahuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَنَّنْ سَيْ يَسَاكٜىٰ غِنَا كَتَنْغَرْ بِرْنِنْ دَاوُدَ وَدَّ تَكٜىٰ بَايَنْ كَتَنْغَ تَڢَرْكُواْ؞ تَا مِيڧٜىٰ دَغَ يَمَّثِنْ رَاڢِنْ غِهُوانْ عَثِكِنْ ݣُورِنْ كِدْرُوانْ ذُوَا ڧُواْڢَرْ كِيڢِ، حَرْ تَثِيغَبَ تَكٜىٰوَيٜىٰ تُدُنْ عُواْڢٜىٰلْ، عِنْدَ عَكَغِنَ شِ دَ ڟَيِ سُواْسَيْ؞ يَكُمَسَا مَنْيَنْ سُواْجُواْجِنْسَ أَدُكْ بِرَنٜىٰنْسَ مَاسُ كَتَنْغَ أَ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan haka sai ya gina garu a bayan garin Dawuda a yammacin Gihon, a kwari har zuwa Ƙofar Kifi, ya kewaye da shi zuwa Ofel, ya gina shi da tsayi sosai. Sa'an nan ya sa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuza.