2 Chronicles 33:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَنْ سَاكٜىٰ سَا أَ ڢِتَرْدَ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَغَ ڧَسَرْدَ نَبَا كَاكَنِّنْسُ بَ، عِدَنْ دَيْ سُكَ لُورَ سُكَ كِيَايٜىٰ دُكَنْ عُمَرْنَنْدَ نَبَاسُ دَ دُكَنْ ڧَٰعِدُواْدِ دَ كُواْيَرْوَرْ دَ بَاوَنَ مُوسَٰى يَعُمَرْثٜىٰسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba zan ƙara fitar da Isra'ila daga ƙasar da na ba kakanninku ba, in dai sun lura, sun kiyaye, sun aikata dukan abin da na umarce su, da dukan shari'a, da dokoki, da ka'idodi da aka bayar ta hannun Musa.”