2 Chronicles 34:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hilkiya tare da waɗanda sarki ya aika, suka tafi suka yi magana da annabiya Hulda, wadda take matar Shallum ɗan Tokhat ɗan Hasra, mai tsaron wurin ajiyar riguna. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
هِلْكِيَ دَ وَطَنْدَ سَرْكِے يَعَيْكَ سُكَ تَڢِے سُيِ مَغَنَ دَ أَنَّبِيَ هُلْدَ؞ عِتَ ثٜىٰ مَاتَرْ شَلُّمْ طَنْ تُواْخَتْ جِيكَنْ هَسْرَ؞ شَلُّمْ نٜىٰ يَنَ لُورَ دَ رِيغُنَنْ عَيْكِ ثِكِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ هُلْدَ تَنَ ذَمَ ثِكِنْ عُرُوشَلِيمَ أَ سَابُوَرْ عُنْغُوَ؞ سَيْ سُكَ بَيَّنَ مَتَ أَبِنْدَ يَڢَرُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hilkiya kuwa tare da waɗanda sarki ya aika suka tafi wurin annabiya Hulda, matar Shallum ɗan Tikwa, ɗan Harhas, mai lura da wurin ajiyar tufafi, tana zaune a Urushalima, a unguwa ta biyu. Suka faɗa mata saƙon sarki,