2 Chronicles 34:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙarƙashin umarninsa aka rurrushe bagadan Ba’al, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu, ya farfashe ginshiƙan Ashera da kuma sassaƙaƙƙun siffofi. Ya ragargaza waɗannan kucu-kucu, ya barbaɗa su a kan kaburburan waɗanda suka miƙa musu hadayu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَسَا مُتَنٜىٰ سُكَ رُشٜىٰ بَغَدَنْ يِنْ سُجَّدَ غَ غُمَكَنْ بَعَلْ؞ يَكُمَ رُشٜىٰ بَغَدٜىٰنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰنْ هَدَايُ دَسُكٜىٰ عَبِسَنْسُ؞ يَڢَرْڢَشٜىٰ غُمَكَنْ أَشٜىٰرَ دَ صِڢُّواْڢِنْ أَلُّواْلِنْ إِتَاثٜىٰنْ دَ عَكَ سَسَّڧَ دَ صِڢُّواْڢِنْ ظُبِے؞ سَيْ يَنِڧَسُ دُكَ سُكَ ذَمَ ڧُورَا؞ سَعَنً يَوَاڟَرْدَ ڧُورَرْسُ أَوُرِنْ كَبَرِنْ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَ مِيڧَ هَدَايُ أَغَرٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka farfashe bagadai na Ba'al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu.