2 Chronicles 34:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ƙone ƙasusuwan firistocin gumaka a kan bagaden da a dā suke miƙa hadayunsu, ta haka ya tsabtacce Yahuda da Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَڧُواْنٜىٰ ڧَسُسُوَنْ ڢِرِسْتُواْثِے نَغُمَكَنْ عَكَنْ بَغَدَنْسُ؞ تَيِنْ حَكَ يَڟَبْتَثٜىٰ يَهُودَ دَ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma ƙone ƙasusuwan firistoci a bisa bagadansu, ya tsarkake Yahuza da Urushalima.