2 Chronicles 34:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya, ya tsarkake ƙasar da haikalin, ya aiki Shafan ɗan Azaliya da Ma’asehiya mai mulkin birni, tare da Yowa ɗan Yowahaz, marubuci, su gyara haikalin Ubangiji Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ شٜىٰكَرَا تَغُواْمَشَا تَݣُوسْ تَمُلْكٍ يُواْسِيَا، بَايَنْدَ يَڟَبْتَثٜىٰ ڧَسَرْدَ كُمَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، سَيْ يَعَيْكِ مُتَنٜىٰ عُكُ دُواْمِنْ سُڠَرَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسَ؞ سُونَيٜىٰنْسُ سُونٜىٰ، شَڢَنْ طَنْ أَظَلِيَ دَ ڠُومْنَنْ عُرُوشَلِيمَ مَيْ سُونَ مَعَسٜىٰيَ دَ مَرُبُوثِ يُواْوَ طَنْ يُواْوَهَظْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, bayan da ya gama tsarkake ƙasar, da Haikalin, sai ya aiki Shafan ɗan Azaliya, da Ma'aseya mai mulkin birnin, da Yowa ɗan Yowahaz, wanda suke magatakarda domin su gyara Haikalin Ubangiji Allahnsa.