2 Chronicles 34:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka tafi wurin Hilkiya babban firist suka ba shi kuɗin da aka kawo cikin haikalin Allah, wanda Lawiyawa masu tsaron ƙofofi sun tattara daga mutanen Manasse, Efraim da dukan raguwar Isra’ila da kuma daga dukan mutanen Yahuda da Benyamin da kuma mazaunan Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنَّنْ عُكُ سُكَ تَڢِے وُرِنْ هِلْكِيَ بَبَّنْ ڢِرِسْتِ، سُكَ بَاشِ كُطِنْ دَ عَكَ كَٰوُاْ عَثِكِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، وَنْدَ لَوِيَاوَا مَاسُ غَادِنْ ڧُواْڢَرْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ سُكَ تَتَّارَ دَغَ مُتَنٜىٰنْ ذُرِيَرْ مَنَسّٜىٰ دَ نَ إِڢْرَيِمْ دَ نَضَغُواْوَرْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ نَدُكَنْ ذُرِيَرْ يَهُودَ دَ تَ بِلِيَامِنُ دَ مَذَوْنَنْ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka zo wurin Hilkiya babban firist, suka ba shi kuɗin da aka kawo a Haikalin Allah, wanda Lawiyawa, masu tsaron ƙofa, suka tattara daga mutanen Manassa da na Ifraimu, daga sauran Isra'ila, da kuma na dukan Yahuza da Biliyaminu, tare da na mazaunan Urushalima.