2 Chronicles 35:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan wannan, suka shirya wa kansu da kuma wa firistoci, saboda firistoci, zuriyar Haruna, suna miƙa hadayun ƙonawa da sashen kitse daga safe har dare. Saboda haka Lawiyawa suka shirya wa kansu da kuma wa firistocin daga zuriyar Haruna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَنَّنْ دُكَ، سَيْ لَوِيَاوَا سُكَ شِرْيَ وَكَنْسُ دَ ڢِرِسْتُواْثِے عَبِنْثِ، سَبُواْدَ ڢِرِسْتُواْثِے، وَتُواْ یَیَنْ هَٰرُونَ، سُنَ تَ عَيْكِ دَغَ سَڢٜىٰ حَرْ دَرٜىٰ، سُنَ مِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا دَ سَاشٜىٰ نَكِڟٜىٰنْ دَبُّواْبِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga baya kuma suka shirya wa kansu da firistoci, saboda firistoci, 'ya'yan Haruna, maza, suna ta hidimar miƙa hadayu na ƙonawa, da kuma na kitse, har dare. Don haka Lawiyawa suka shirya wa kansu abinci, suka kuma shirya wa firistoci, 'ya'yan Haruna, maza.